Najeriya: Matasa Sun Fara Zanga Zanga Kan Tsadar Rayuwa

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Fadin Najeriya

Matasa a sassan Najeriya sun fara gudanar da zanga zanga kan tsadar rayuwa da sauran matsaloli da suke addabar kasar.

Matasan dai sun fito a kan manyan titunan biranan kasar, kama da Legas, Kano, Abuja, Borno da sauran su.

'Yan sandan Najeriya lokacin Zanga-zangar tsadar rayuwa

Matasan dai suna kokawa kan tsadar man fetur, wutar lantarki, kayan masarufi da dai sauran su, inda suke ta kiraye-kiraye da gwamnatin ta dauki matakai na kawo mafita daga wannan mawuyacin hali da al’ummar kasar take fuskanta na fatara da talauci.

Gwamantin tarayyar kasar ta nemi matasan da su kara ba ta lokaci domin tuni ta fara daukan matakai don magance wadannan matsaloli.

Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Sai dai matasan sun ce manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu ne da ta dauka suka kara jefa kasar cikin wannan hali na matsi.

Tun a ranar 29 ga watan Mayu 2023 ne dai Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin dalar Amurka.

Amma gwamnatin tarayyar ta ce manufofinta sun fara aiki, don haka mutane su kara hakuri kafin komai ya kankama.