Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Yi Watsi Da Kiraye-Kirayen Zanga-Zanga, Sakataren Gwamnati Ga ‘Yan Najeriya


Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Sanata George Akume
Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Sanata George Akume

A yau Laraba, sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Sanata George Akume, ya yi kira ga ‘yan Najeriya a kan kada su shiga cikin zanga-zangar gama garin da aka tsara yi a kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Akume ya yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai a Abuja a jajibirin zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya Abuja.

A cewar sakataren gwamnatin Najeriyar, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na iya bakin kokarinta wajen warware dimbin matsalolin dake addabar kasar.

Ya ci gaba da cewar, “don haka muna kira ga ‘yan Najeriya daga kowace kabila ko addini, yaro ko babba, maza da mata dasu yi watsi da kiraye-kirayen gudanar da zanga-zanga a kan yunwa ta hanyar baiwa zaman lafiya da ci gaba mahimmanci.”

Ya kuma bayyana fatan cewar, halin kunchin da ‘yan Najeriya ke fuskanta zai zama tarihi duba da dimbin matakan da gwamnatin tarayya ke dauka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG