Kakakin rundunar mayakan kasar Chadi Janar Azem Bermandoa Agouna shi ne ya bayar da sanarwar mutuwar shugaban kasar Chadi Idriss Deby ta kafafen yada labaran gwamnati.
Ya ce shugaba Idriss Deby ya rasu ranarTalata 20 ga watan Afrilu, a daidai lokacin da yake kokarin kare martabar kasa a fagen daga.
Jajircewar shugaba Deby akan batun yaki da ta’ddanci ya sa masana sha’anin tsaro irin su Alkassoum Abdourahaman ke kallonsa da kima.
Idriss Deby wanda ya rasu kwana daya bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a karo na shida, ya yi rayuwa irin ta mutunen da za a yi wa taken ba yabo ba fallasa, a cewar Abdou Idi na kungiyar FSCN.
Karin bayani akan: Idriss Deby, Boko Haram, kasar ta Chadi, da Chad.
Mutuwar Idriss Deby wani babban gibi ne ba wai ga kasashen Sahel kawai ba, matsala ce da ka iya shafar nahiyar Afrika baki daya.
Marigayin ya dare kujerar shugabancin Chadi a ranar 4 ga watan Disambar 1990 bayan da ya hambarar da gwamnatin Hissene Habre daga karagar mulki, kuma dukkan wasu yunkurin kifar da gwamnatinsa ya citura.
Sai dai wannan mutawa ta shugaban ta zo wa duniya cikin yanayi na bazata tare da babban darasi.
Idriss Deby mai shekaru 69 na daga cikin shugabannin kasashe da suka halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Nijar, Mohammed Bazoum, a ranar 2 ga watan Afrilu 2021.
A tsakiyar watan Maris, marigayin ya ziyarci wasu sojan kasar Chadi 1200 wadanda suka yada zango a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, akan hanyarsu ta zuwa iyakar Mali da Burkina Faso da kuma Nijar domin aikin tsaro karkashin rundunar kasashen G5 Sahel.
A karshen shekarar 2019 zuwa farkon 2020 ya jagoranci wata gagarumar rawar dajin sojin Chadi a kewayen yankin tafkin Chadi, inda suka yi nasarar kakkabe ‘yan ta’addar Boko Haram a kalla 1000.
A shekarar 2008 daukin da ya samu daga kasar Faransa ya bashi damar murkushe wani yunkurin ‘yan tawaye, sai dai kuma alamu na nunin Idriss Deby ya mutu ne a wani lokacin da ake fuskantar tsamin dangantaka da shugabanin Faransa kasar da ta yi wa Chadi mulkin mallaka, ya yin da a daya bangaren ‘yan tawayen kungiyar FACT ke barazanar kutsawa birnin N’djamena a yanzu haka.
Tuni aka kafa wani kwamitin rikon kwarya mai alhakin tafiyar da lamuran mulkin kasar a karkashin shugabancin daya daga cikin ‘ya yansa Janar Mahamat Idriss Deby mai shekaru 37 a duniya, wanda har mutuwar mahaifinsa yakeya ke jagorancin rundunar dogarawan fadar shugaban kasa.
Your browser doesn’t support HTML5
Sabon Shugaban Mulkin Sojin Chadi A Wajen Jana’izar Mahaifinsa
An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas