Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Da Bazoum Sun Yi Buda Bakin Azumi A Abuja


Buhari da Bazoum sun yi buda baki a tare.
Buhari da Bazoum sun yi buda baki a tare.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gudanar da buda baki azumin Ramadan da takwaransa na Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, wanda ya kai masa ziyara a Abuja.

Shugabannin biyu sun gaudanar da sallar Magrib a masallacin fadar shugaban kasa ta Aso Rock, kafiun daga bisani suka zarce zuwa babban dakin taro inda suka ci abincin buda baki.

Mohamed Bazoum na kan ziyararsa ta farko ne a Najeriya jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin sabon zababben shugaban kasar Nijar a ranar 2 ga watan nan na Afrilun shekarar 2021.

Buhari da Bazoum sun yi buda baki a tare
Buhari da Bazoum sun yi buda baki a tare

Tun kafin buda bakin, shugabannin biyu sun gudanar da wani taro a kadaice, inda aka ce sun tattauna wasu muhimmam Abubuwa da suka shafi dangantaka da al’ummomin kasashen Najeriya da Nijar, da suka hada da tsaro da kuma tattalin arziki.

Buhari da Bazoum sun yi buda baki a tare
Buhari da Bazoum sun yi buda baki a tare

Wata sanarwa da mai Magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina ya fitar, ta ce shugabannin biyu sun yi alkawarin daidaita al’amura a yankunan kasashensu domin amfanin jama’arsu.

Sanarwar ta ruwaito shugaba Buhari yana cewa “’Yan Najeriya da ‘yan Nijar al’ummomi ne da suke tarayya akan al’adu da harshe da ma yanayin tsarin rayuwa. Mun yi iyaka ta tsawon kilomita 1,500, don haka ba yadda za’a yi mu yi watsi da juna.”

Buhari ya gana da Bazoum a Abuja
Buhari ya gana da Bazoum a Abuja

Da ya juya kan sabon shugaban kasar ta Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, Buhari ya ce “Kai ba bako ba ne, ka dade a cikin tsarin. Abin da kawai ba ka taba yi ba shi ne shugaban kasa, ta yanzu ka zama shugaban kasar.”

Buhari ya kuma jinjinawa shugaba Mahamadou Issoufou da ya sauka, akan “fahimta da jajircewarsa, wadanda suka taimaka wajen daidaita al’amura a Nijar da ma yankin baki daya.”

Akan haka ya yi kira ga Bazoum da ya yi kokarin dorewa da kyakkyawan tubali da Issoufou ya gina, domin wanzar da dimokaradiyya a kasar ta Jamhuriyar Nijar da nahiyar Afirka.

Buhari ya tarbi Bazoum a Abuja
Buhari ya tarbi Bazoum a Abuja

Shi ma a na shi jawabin jim kadan bayan ganawar ta sirri, sabon shugaban Nijar Bazoum Mohamed ya ce kasashen 2 na Najeriya da Nijar suna bukace da juna, don haka akwai bukatar kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu.

Ya ce yadda ‘yan Najeriya suke rugawa neman mafaka a Nijar a duk lokacin da aka sami harin ‘yan ta’adda, shi ya nuna cewa akwai bukatar hadin kai da aiki tare domin shawo kan matsalolin da ke addabar al’umma.

Ziyarar ta Bazoum a Najeriya, ita ce ziyara ta farko da ya kai a wata kasa a hukumance, bayan kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Nijar a ranar 2 ga watan Afrilu.

Idan za’a iya tunawa dai Bazoum ya karbi mulki ne a hannun tsohon shugaba Mahamed Issoufou, karon farko da aka sami nasarar mika mulki daga gwamnatin dimokaradiyya zuwa wata sabuwar zababbiyar gwamnatin dimokaradiyya a tarihin kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG