Mutum 5 Sun Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Sama A Nepal

Nepal

Mutum biyar da ke cikin wani jirgi mai saukar ungulu sun mutu a wasu tsaunuka da ke arewa maso yammacin babban birnin Nepal a cewar hukumomi.

Krishna Prasad Humagai, jami'in gwamnati a gundumar Nuwakot, ya ce an ciro gawarwakin maza hudu da wata mata daga cikin tarkacen jirgin.

Kathmandu, Nepal

Jami’in ya ce jami’an ‘yan sanda da sojoji masu aikin ceto sun isa yankin, sannan an kuma aike da jirage masu saukar ungulu guda biyu don taimakawa wajen aikin ceto.

Wurin da hatsarin ya afku a yankin Suryachaur ne, wanda ke arewa maso yammacin Kathmandu, kuma yana kan wani dutse da yake lullube da daji.

Nepal

Jirgin mai saukar ungulu ya tashi daga filin jirgin saman Kathmandu ne da karfe 1:54 na rana lokacin kasar kuma yana kan hanyar zuwa garin Syaprubeshi.

-AP