Jirgin sojan da ke dauke da Chilima mai shekaru 51 da kuma wasu 9 ya bace a ranar Litinin din da ta gabata, bayan da ya kasa sauka a birnin Mzuzu da ke arewacin kasar sakamakon mummunar yanayi, inda aka ce ya koma Lilongwe babban birnin kasar.
"Rundunar bincike da ceto sun gano jirgin inda gaba dayansa ya lalace ba tare da wani mai rai ba, saboda duk fasinjojin da ke cikin jirgin sun mutu sakamakon hatsarin," in ji shugaban Malawi Lazarus Chakwera yayin da yake jawabi ga al'ummar kasar.
"Kalmomi ba za su iya kwatanta irin takaicin wannan lamarin ba," in ji shi, yana mai bayyana hatsarin a matsayin "mummunan bala'i."
Hotunan da wani mamban tawagar sojojin da suka ceto ya raba wa AFP ya nuna jami'an soji a tsaye a kan wani tudu mai hazo kusa da tarkacen jirgin.
Kwamandan sojojin kasar Janar Paul Valentino Phiri, ya ce wasu kasashe da suka hada da makwabtan Malawi, sun taimaka wajen binciken, tare da tallafin da suka hada da jirage masu saukar ungulu da jirage marasa matuka.
Dandalin Mu Tattauna