Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Jirgin Sama A Kasar Nepal Ya Kashe Akalla Mutane 68


Masu agaji da mutane sun taru a wajen hatsarin jirgin sama a Nepal, Jan. 15, 2023/hoto daga social media. (Naresh Giri/via Reuters)
Masu agaji da mutane sun taru a wajen hatsarin jirgin sama a Nepal, Jan. 15, 2023/hoto daga social media. (Naresh Giri/via Reuters)

Wani hatsarin jirgin sama ya kashe mutane akalla 68, a cewar hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Nepal.

WASHINGTON, D.C. - Wani jirgin saman fasinja na yankin dauke da mutane 72 ya fada cikin wani kwazazzabo, yayin da yake sauka a wani sabon filin jirgin sama da aka bude a garin shakatawa na Pokhara a ranar Lahadi, a hatsarin jirgin sama mafi muni a kasar cikin shekaru talatin.

Masu aikin ceto da masu kallo da dama ne suka yi cunkoso a kusa da wani tudu mai gangara da yammacin ranar Lahadi, yayin da masu aikin ceto ke tsegunta tarkacen da ke gefen dutsen da kuma kwarin da ke kasa.

Wani mazaunin yankin, Bishnu Tiwari, wanda ya garzaya wurin da hatsarin ya faru, domin taimakawa wajen gano gawarwakin, ya ce aikin ceto ya ci tura saboda kaurin hayaki da kuma wutar da ta mamaye jirgin.

“Gobarar ta yi zafi sosai har ba za mu iya zuwa kusa da jirgin ba. Na ji wani mutum yana kukan neman taimako, amma saboda wuta da hayaki ba mu iya taimaka masa ba,” in ji Tiwari.

Kawo yanzu dai ba a bayyana abin da ya haddasa hatsarin ba.

-AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG