Dubban ‘yan Misra sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da gazawar jami’an tsaro wajen hana tashin hankali a wajen gasar kwallon kafa da ya kai ga mutuwar akalla mutane 74 da kuma raunatar daruruwar mutane a birnin Port Sa’id da ke arewacin kasar.
Wasu masu zanga-zangar sun taru a yau dinnan Alhamis a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin al-Kharira a sa’ilinda wasu kuma su ka yi maci zuwa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da ke kusa da wurin, a inda ‘yan sandan kwantar da tarzoma su ka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa su.
Wani taron jama’a kuma ya yi ta ihun gwale gwamnatin ta mulkin soja a tashar jirgin kasar birnin al-Khahira ta inda wadanda su ka tsira daga yamutsin na ranar Laraba ke isowa gida, wasunsu da raunuka.
Firayim Minstan Misra da soji su ka nada wato Kamal al-Ganzuri y ace gwamnati ta rushe Hukumar Kwallon Kafar Misra ta kuma dakatar da gwamnan Port Sa’id da kuma shugabannin bangarorin tsaro a matsayin martanin faruwar wannan bala’in, wanda ya na daya daga cikin mafiya muni a tarihin wasannin motsa jiki.