Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane 9 a tashin hankalin kwana biyu a Misra


Masu zanga-zanga kenan ke fafatawa da jami'an tsaro a Misra
Masu zanga-zanga kenan ke fafatawa da jami'an tsaro a Misra

Mummunan fada tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga

Mummunan fada tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga ya sake dabaibaye kasar Misra a rana ta biyu. An hallaka akalla mutane 9 aka kuma raunata akalla wasu 300 a tashe-tashen hankulan na kwanaki biyu.

Sojoji sun yi ta fafara tare da dukan ‘yan zanga-zanga masu jifarsu da duwatsu da ke kokarin tattaruwa a Dandalin Tahrir da ke birnin al-Khahira a jiya Asabar.

Wani wakilin Muryar Amurka ya ga ‘yan sanda na bugun masu zanga-zanga da kulaken karfe yayin da su ke kokarin haduwa don yin kururuwar neman a kawo karshen mulkin soji. A wasu lokutan ma ‘yan zanga-zanga sun yi ta girke shingaye don kare kansu.

Tashin hankalin ya auku bayan zango na biyu na zaben Majalisar Dokoki, wanda shi ne zaben kasar na farko tun bayan murabus din Shugaba Hosni Mubaraka a cikin watan Fabrairu.

XS
SM
MD
LG