Alkalin kotun shari’ar masu aikata laifukan shige da fice a Amurka, ya bada umarnin maida wani dan kasar Liberia zuwa kasar da ya fito saboda zargin da ake masa na aikata laifin kisan kai da kuma cusa yara aikin soja a lokacin yakin basasar kasar Liberia.
Alkalin kotun shari’ar laifukan shige da fice ta Amurka, yace an sami George Boley mai shekaru 62 da haihuwa da laifin kisan kai, don haka bashi da sauran ‘yancin ci gaba da zama a Amurka.
Dan George Boley, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na “Associated Press” cewa alkalin kotun yayi watsi da duk muhimman shaidun da mahaifinsa ya gabatar a gaban kotun.