Mutane Fiye Da Miliyan 371 Ne Ke Fama Da Ciwon Sukari A Duniya

Tambarin Ranar ciwon sukari ta Duniya

Hukumomin jahar Naija a arewacin Najeriya sun yi bikin ranar ciwon sukari ta duniya
A jahar Naija da ke arewacin Najeriya an gudanar da bikin ranar duniya ta ciwon sukari kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta yi tanadi kowace shekara a ranar goma sha hudu ga watan goma sha daya domin maida hankali kan masu wannan cuta da kuma kara fadakar da jama'a a kan cutar. Wata kididdigar da aka gudanar ta nuna cewa a duniya mutane sama da miliyan dari uku da saba’in da daya ne ke shan wahalar wannan ciwo na sukari. Dakta Idris Muhammad shi ne shugaban kungiyar masu fama da cutar a jahar Naija, a tattaunawar su da wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari, Dakta Idris Muhammad ya ce wannan rana ta na da muhimmancin gaske wajen tunatarwa da kuma fadakarwa.

Your browser doesn’t support HTML5

Bikin ranar duniya ta fadakarwa game da ciwon sukari - 2:26