Wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, yace shugabannin na APC, wadanda suka hada da janar Muhammadu Buhari, da Bola Ahmed Tinubu, da tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya ta Najeriya, Aminu Bello Masari, sun tattauna da tsoffin shugabannin cikin sirri.
Daga bisani, janar Babangida ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara ta su, yana mai fadin cewa tilas bisa al'ada a yi marhabin da duk wanda yazo da wata shawara ta hanyar da za a iya warware matsalolin kasa.
Shugaban jam'iyyar ta APC na riko, Cif Bisi Akande, yace sun kai ziyarar ce domin neman hadin kan wadannan tsoffin shugabannin kasa.
Sai dai kuma, wani shugaban jam'iyyar ta APC, Faruk Adamu Aliyu, yace hukumar zaben Najeriya, INEC, tana neman taka musu burkin wannan rangadin da suke yi, inda ta aiko musu da takardar cewa abinda suke yin ya saba ma doka don tamkar yakin neman zabe ne.
jami'in yace zasu nazarci wannan takarda ta hukumar INEC idan sun koma Abuja domin su ga irin abinda doka ta ce kan wannan yunkurinsu na kafa sabuwar jam'iyyar a kan kafafunta.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari...