A wata sanarwar da babbar jami’ar hukumar yaki da ayyukan ta’addancin kasa da kasa ta Amurka Lisa Monaco, ta bayar jiya laraba na cewa, kungiyoyi biyun da aka ambata sune Ummul Haba’isin kisan da ake yiwa dubun dubatar ‘yan Nigeria a yankin Arewa maso gabashin Nigeria. Babbar jami’ar ta kara da cewa kazalika, ba wanda za’a dorawa hakkin yawan kai hare-haren da ake yi kan Mujami’u daMasallatai da wuraren taruwar jama’a im banda kungiyar Boko Haram.
Babbar jami’ar ta kuma azawa kungiyar Boko haram laifin shirya kai hare-haren da Boko haram ta kaiwa gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya a Abuja Nigeria, inda aka halaka mutane 21.