Har yanzu, babu wata alamar dake nuna cewa 'yan PDP-Sabuwar zasu ci gaba da zama a PDP ne ko kuma zasu karbi goron gahyyatar shiga wata jam'iyyar dabam.
Tafidan na Bodinga, yace akwai takaici ganin cewa wasu jam'iyyu su na can su na ta yakin neman zabe yayin da su a PDP suke ta fada. Yace shugaban PDP-Tsohuwa, Bamanga Tukur, mutum ne wanda a dalilin hakurinsa jam'iyyar ta kai matsayin da take.
Sai dai kuma wani dan NEPU-Sawaba, Hussaini Gariko, ya shawarci gwamnonin dake tawayen da su ci gaba da zamewa jam'iyyar PDP-Tsohuwa kadangaren bakin tulu, a kar ka a kar tulu, a kyale ka, ka bata ruwa.
Yace muddin ba a biya musu bukatunsu ba, to sake hadewa da PDP-Tsohuwa babban hatsari ne ga wadanda suke yin tawayen.
Ga cikakken bayani a bakin Nasiru Adamu el-Hikaya.