Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Makiyaya Ta Miyetti Allah Ta Koka Kan Barayin Shanu Dhttp://voa.pangea-cms.com/publisher/img/articleIcons/icon1.gifaga Filato


Yara suke wasa da shanu a jihar kaduna.
Yara suke wasa da shanu a jihar kaduna.

Akalla an kashe mutane goma aka sace dabbobi fiyeda dubu biyu cikin sama da wata daya.

Kungiyar Miyetti Allah ta fulani makiyaya a jihar Taraba ta yi kira ga mahukunta a jihohin Taraba da Flato su dauki mataki domin magance yawan hare hare da suke zargi ana kawo musu daga makwabciyar jiha watau Flato.

A wani taron manema labarai da shugaban kungiyar Alhaji Mafindi Umar Danburam ya kira a Jalingo, yace daga ranar 10 ga watan jiya zuwa yanzu an kashe akalla mutane 10 aka kuma sace dabbobi fiyeda dubu daga jihar.

Mafindi ya aza laifin haka kan kungiyar tsoffin sojoji daga jihar Falto wadanda suke tsallakowa su shiga jihar Taraba, musamman a Ibbi dake kan iyaka, su aikata barna. Ya lura cewa gwamnatocin jihohin biyu ba sa daukan matakai na shawo kan wannan lamari.

Amma da yake magana kan wannan batu, mukaddashin gwamnan jihar Taraba Alhaji Garba Umar, yace gwamnatinsa ta zauna da takwararta ta jihar Flato inda suka cimma matakai na shawo kan wannan rikici.

Kamar yadda zaku ji cikin wannan rahoto da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG