Wasu mutane biyu, ciki har da wani yaro dan shekara biyar sun jikkata bayan da wata mata ta bude wuta kan wata babbar cocin fitaccen Paston da ake kira Joel Osteen a birnin Houston da ke jihar Texas a Amurka, daya daga cikin wuraren ibada mafi girma a kasar, a cewar 'yan sanda ranar Lahadi.
Matar dai na dauke da bindiga a lokacin da ta shiga cocin tare da wani yaro kusan karfe 2:00 na rana agogon GMT, kamar yadda shugaban ‘yan sandan Houston Troy Finner ya shaida wa taron manema labarai.
A lokacin da ta isa cocin, wacce a da babban filin wasanni ce da mutane kusan 16,800 ke taruwa a cikinta, ta fara harbi, in ji Finner, amma jami'an 'yan sanda da ke aikin tsaro a wurin suka harbe ta har lahira.
"An harbe wani yaro dan shekara biyar kuma yana cikin mawuyacin hali a asibiti," in ji Finner, yayin da wani mutum mai shekaru 50 na jinyar harbin bindiga da ya samu a kafa.”
Hare-hare kan jama'a sun zama ruwan dare a Amurka, inda ake da bindigogin da suka fi jama’a yawa kuma kusan kashi uku na Amurkawa manya sun mallaki bindiga.
Osteen, wanda ake watsa shirye-shiryen sujada a cocinsa kai tsaye ga miliyoyin mutane a duk mako, kuma wanda bai tsoma cocin cikin harkokin siyasa, ya ce harin ya “tada masa hakalinsa sosai.”