Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Wani Mai Zanga Zangar Mutunta Bakar Fata Har Lahira


Shugaban Kasar Aurka Donald Trump
Shugaban Kasar Aurka Donald Trump

‘Yan Sanda sun ce an harbe mutum daya ranar Asabar a birnin Portland dake jihar Oregon yayin da masu zanga zangar neman a mutunta rayukan bakaken fata suka karu a titunan kasar da masu goyon bayan shugaba Donald Trump.

Magoya bayan shugaban na Amurka sun fito cike da daruruwan manyan motoci a birnin, dayan su na koyon harbi daga budandun motoci yayin da masu zanga zangar kuma suka dinga jifansu.

‘Yan sanda sun fitar da sanarwa cewa, jami’ai sun ji harbin bindigogi kuma sun gano wani mutun da aka harba a kirji. Jami’an kiwon lafiya sun tabbatar ya mutu bayan da suka gwada numfashin sa.

Da safiyar Lahadi shugaban 'yan sandan Portland, Chuck Lovell ya fadi cewa,

“Ba mu aminta da wannan tashin hankali ba kuma muna aiki tukuru domin gano wanda ko wadanda ke da alhakin aikata hakan.”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG