WASHINGTON, D. C. - Fashewar ta faru ne a ranar Litinin a karamar hukumar Emohua da ke kudancin jihar Rivers, inda ake yawan samun haramtattun matatun mai. Mazauna yankin sun ce akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya karu, saboda wasu gawarwakin da yawa sun kone kurmus kuma wasu da dama sun jikkata.
‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin amma ba su bayar da cikakken bayanin abin da ya faru ba. Mazauna yankin sun ce akasarin mutanen da suka mutu sun yi aiki a haramtacciyar matatar man da ke kauyen na Rumucholu.
Ma’aikatan da ke wurin suna tace mai ne da suka samo daga wani bututun mai da aka fasa a cewar Chima Avadi, wani mai fafutuka a yankin. “Idan suka kwaso man daga bututun, sai su kai shi inda suke girki. Da haka ne wuta ta kama a wurin,” in ji Avadi.
Ya ce ana jinyar mutane da dama a asibitoci. Wata mata mai juna biyu na daga cikin mutane 15 da aka tabbatar da mutuwarsu, a cewar wata sanarwa da cibiyar kare matasa da muhalli ta Youths and Environmental Advocacy Centre ta fitar.
Samun fashe-fashe a matatun man da aka bude ba bisa ka’ida ba ya zama ruwan dare a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur amma kuma yake fama da talauci, inda akasarin cibiyoyin man kasar ke fuskantar matsalar satar mai.
Yawancin lokuta masu kauce wa bin ka'ida dake guje wa masu sa ido ne ke kafa matatun mai a wuraren dake wajen gari. Ma’aikatan da ke aiki a irin wadannan wuraren ba kasafai suke bin ka’idojin kariya ba, lamarin da ke janyo tashin gobara akai-akai, ciki har da wata gobara da ta faru a jihar Imo a shekarar da ta gabata wadda ta kashe mutane sama da 100.
-AP