Wata gobara da ta shi a gabar ruwan garin Calabar dake jihar Cross River yayin da wani jirgin mai ke sauke kayansa, ta halaka mutane 9 a cewar jami’an tsaron jihar.
“A halin yanzu zan iya ce maka mutum 9 suka rasu a sanadiyar wannan.” In ji Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Cross River Hafiz Inuwa.
Bayanai sun yi nuni da cewa wasu mutane ne suka fasa bututun man dake aikewa da danyan man zuwa tankuna, lamarin da ya haddasa tashin gobarar.
Ko da yake kwamishinan ‘yan sandan bai bayyana abinda ya haifar da fashewar ba, amma ya ce an ga gawar wani mutum da bai kamata a ce tana wurin ba.
“A wurin da ya fara tsiyayar nan (mai) akwai ma’aikaci na wani kamfani daban, shi dai ba shi da dalilin da ya sa yake wannan wurin an ga gawarsa kuma ba ta wani kone ba.” In ji kwamishina Inuwa.
Sai dai wasu da hadarin ya auku a idonsu, sun ce adadin mutanen da suka mutu bayan aukuwar fashewar ya haura abinda ‘yan sandan suka fada inda ya yi karin haske kan yadda bututun ya fashe.
“Hakiki mutane da dama sun mutu, ni kaina na ga gawarwaki kamar guda 16 zuwa 20, wasu kuma sun fada ruwa domin cecen rayukansu, kuma har yanzu ba a ga gawarwakinsu ba.” In ji Barrister Musa Mai Goro, mai bai wa gwamnan jihar Cross River shawara kan harkar baki.
Sai dai kwamishinan ‘yan sanda Inuwa ya ce ya tuntubi asibitin dake kula da wadanda hadarin ya rutsa da su, an kuma tabbatar mai da cewa mutane tara ne suka rasu.
“Bayan mutum taran da suka rasu muna da wajen mutum tara a kwance a asibiti, idan wani ya sake rasuwa babu mamaki.”
Wasu majiyoyin sun ce adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya haura 30 yayin da wasu ke ikirarin 50.
Mai Goro ya kuma ya yi karin bayani kan abinda ya haddasa gobarar inda ya ce barayin mai ne suka haddasa ta.
“Shi bututun da ake sauke danyan-man ake zubawa manyan-manyan tankunan sai ya samu matsala ya dan fashe…sai man ya fara kwarara, sai masu kokarin su saci wannan mai suka zo da bokatai suka fara kwasa, to ana cikin haka kawai sai wuta ta kama.”
Matsalar fasa bututun domin satar mai ba sabon abu bane a yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya, inda ‘yan bindiga kan yi amfani da nakiyoyi wajen fasa shi.
Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Lamido Abubakar Sokoto domin jin karin bayani:
Facebook Forum