Mutane 780,000 Ne Suka Rasa Matsugunansu A Mozambique Sakamakon Tashe-tashen Hankula - MDD

Mutane 780,000 Ne Suka Rasa Matsugunansu A Mozambique Sakamakon Tashe-tashen Hankula - MDD

Babban jami’in ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani sabon gargadi yau Alhamis cewa sama da mutane 780,000 suka rasa matsugunansu a Mozambique, mafi yawansu saboda tada kayar baya na tsawon shekaru bakwai da kungiyar jihadi ta yi wanda ya jefa arewacin kasar cikin rudani.

WASHINGTON, D. C. - Filippo Grandi, babban kwamishinan MDD mai kula da 'yan gudun hijira, ya kai wata ziyara a lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar Mozambique, inda wata kungiyar da ke da alaka da kungiyar IS ta ke kai hare-hare a kan al'ummomi tun daga shekarar 2017, inda aka tilastawa mutane miliyan 1.3 barin gidajensu domin kubuta daga kashe-kashe da fille kawuna.

Wasu Da Suka Rasa Matsugunansu A Mozambique Sakamakon Tashe-tashen Hankula

Kimanin 600,000 sun koma gida, inda suka tarar da ruguzazzun al'ummomin da aka lalata dukkan gidaje, kasuwanni, coci-coci, makarantu da wuraren kiwon lafiya.

Ziyarar Grandi ta zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar sabbin hare-hare da kungiyar IS ke kaiwa a kasar Mozambique a garin Cabo Delgado tun daga watan Janairu bayan samun ‘dan kwanciyar hankali a shekarar 2023.

Wata Mata Da Yaranta Da Suka Rasa Matsugunansu A Mozambique Sakamakon Tashe-tashen Hankula

Hare-haren sun haifar da sabbin rashin matsugunai ga mutane 80,000, wanda ya sa adadin mutanen da aka tilastawa barin gidajensu da ƙauyuka kuma a halin yanzu sun yi gudun hijira daga Mozambique sama da kashi uku bisa huɗu na miliyan ɗaya, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu kungiyoyin agaji sun yi kiyasin cewa adadin mutanen da aka tilastawa barin kauyukansu saboda tashe-tashen hankula a arewacin kasar tun daga watan Janairu ya haura sama da 100,000.

Grandi ya yi kira da a "ci gaba da sa hannu daga kasashen duniya" don taimakawa Mozambique, tare da shirin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a kasar da ke kudancin Afirka mai fuskantar gibi a kudade.

Majalisar Dinkin Duniya na bukatar dala miliyan 400 don taimakawa mutane a Mozambique a wannan shekarar kadai kuma ta samu alkawuran kashi 5% na kudaden da ake bukata, in ji Robert Piper, mai ba da shawara na musamman kan 'yan gudun hijirar ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres.

-AP