A watan Nuwamba, kungiyoyi masu dauke da makamai sun sha kai hari a kauyukan jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya. Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana fargaba kan yawaitar hare-haren, da tsananinsa da kuma rashin tausayin hare-haren.
Ba a san tashin hankali ba a wannan yanki. Sai dai abun da ba za a rasa ba na rikice-rikecen kabilanci tsakanin manoma da makiyaya da kan barke wanda kuma ya karu sakamakon canjin yanayi.
Amma wadannan rikice-rikicen ba su yi barna ba kamar hare-haren ta'addanci na baya-bayan nan da ake kai wa kauyuka.
Kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Boris Cheshirkov ya ce 'yan gudun hijirar Najeriya da ke isa Nijar na ba wa ma'aikatan agaji cikakkun bayanai masu ban tsoro game da halin da suke ciki. Sun ce kashe-kashe da sauran cin zarafi ne ya sa suka tsere daga gidajensu.
"Hakika, 'yan gudun hijirar da ke zuwa suna gaya wa ma'aikatanmu cewa suna kiran su 'yan fashi. Suna daukar mutane, suna garkuwa da su don neman kudin fansa. Suna wawashe gidaje da kauyuka.”
Cheshirkov ya ce akasarin ‘yan gudun hijirar mata ne da kananan yara. Yawancin, in ji shi, suna zaune ne da al’ummomin yankin a kauyuka 26 da ke fadin Bangui, yankin karkara a yankin Tahoua na Nijar. Ya ce yankin ya riga ya karbi 'yan Najeriya 3,500.
Ya ce hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar hukumomin Nijar na yin rajistar sabbin bakin haure tare da ba su agajin gaggawa. Ya bayana ana bukatar matsuguni, abinci, ruwa da kiwon lafiya cikin sauri.
Haka kuma hukumar ta UNHCR ta kafa zamanta a jihar Sokoto domin taimakawa mutanen da tashin hankalin ya raba su da muhallansu.
Yanzu haka dai Nijar na karbar 'yan gudun hijira sama da 200,000 daga Najeriya. Hukumar ta UNHCR ta ce kokarin jin kai na mayar da martani ga dimbin bakin hauren na da matukar hadari.