A yau ne aka wasu saka iyalai a cikin jirgi daga Athens babban birnin kasar Girka zuwa wani dan karamin gari mai arziki da ake kira Luxemburg. Fiye da ‘yan gudun hijira Dubu Dari Biyar Da Tamanin ne suka fantsama cikin kasar girka da nufin kutsawa kasashen Turai masu arziki.
A watan Satumbar bana ne Kungiyar Tarayyar Turan ta amince da jigilar kai ‘yan gudun hijirar na kan iyakar Tarayyar Turai zuwa kasashen da ke da yalwar basu matsuguni. Iyalan na ranar larabar sune iyalan farko da aka fara wannan tsarin da su.
Haka kuma a ranar Larabar ta yau ne jami’an kasar Hungary suka amince da karbar bincike daga kasar Austria game da mutuwar wasu ‘yan gudun hijira guda 71 da aka dankare su a cikin babbar mota mai na’urar sanyi suka kuma mutu.
Matasalar mutuwar da ta zama daya daga cikin misalan hatsarin da ke tattare da safarar bil’adama a duniya, musamman a wannan lokaci da Turai ke fama da kwararar bakin haure.