Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunwa A Kasashen Afirka - UNICEF


Mutanen da yaki ya rabasu da muhallansu suna jiran taimakon abinci
Mutanen da yaki ya rabasu da muhallansu suna jiran taimakon abinci

A wannan shekarar fiye da kowace shekara, yunwa zata addabi kusan kowane sassan kasashen Afirka saboda wasu dalilai, da yawancinsu, ba na Allah da Annabi ba ne

Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice ta riga ta sanarda duniya cewa wasu sassan Sudan ta Kudu sun fada cikin fari tare fama da karancin abinci mai gina jiki, kuma haka lamarin yake a wasu kasashen dake wannan yankin na nahiyar.

Dalilai da yawa suka haddasa fari da karancin abinci amma dalili mafi muni shi ne yawan yake yake dake hana al'umma zama wurarensu cikin lumana su samu su yi noma.

Idan an samu fari cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya akwai yiwuwar fitowa daga ciki saboda kokarin da mutane zasu yi na ganin sun kaucewa bala'in yayinda damina mai zuwa. Amma duk inda aka cigaba da yaki da tashin hankali komin kyawon damina babu abun da mutane zasu iya yi su yi shuka su samu abinci. Ana ta kai ta kai ba'a ta kaya. Muddin aka cigaba da yaki da ta'adanci babu wata masalaha da mutane zasu samu dangane da abinci. Hakan ya faru a arewa maso gabashin Najeriya musamman a jihar Borno inda mutane suka kwashe shekaru da dama ko kwayar hatsi basu noma ba.

Hukumar raya yara wato UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta kiyasta cewa cikin wannan shekarar kawai yara sama da miliyan daya da dubu dari hudu ne zasu rasa rayukansu sanadiyar matsaniyar yunwa a kasashen Najeriya da Sudan ta Kudu da Somalia da Yemen. Duk kasashen suna cikin yaki ne, walau na kabilanci ko na ta'adancin masu ra'ayin rikau bisa tasu fahimtar addininsu.

UNICEF tace abun da zai taimaka da kuma hukumar take so shi ne a kowace kasa inda ake yaki wadanda suke karawa da juna su bata damar kai ga yaran dake bukatan abinci da magunguna cikin gaggawa.

Daya daga cikin yaran da yuwa ta addabesu a jihar Bornon Najeriya sanadiyar yakin Boko Haram
Daya daga cikin yaran da yuwa ta addabesu a jihar Bornon Najeriya sanadiyar yakin Boko Haram

A kasar Sudan ta Kudu UNICEF nada cibiyoyi 600 inda zata iya bada taimako amma yawancin masu bukatar taimakon basa iya zuwa cibiyoyin saboda rikici. Yara na mutuwa kullum kuma ya kamata mu kai garesu cikin gaggawa mu cetosu daga mutuwa inji jami'an UNICEF.

Cikin rahoton Hukumar Abinci WFP ta Majalisar Dinkin Duniya an kiyasta cewa akwai mutane fiye da miliyan 12 a kusiryar Afirka da Kudancin Afirka da suka dogara kacokan ga taimakon abinci daga hukumar ko wasu kungiyoyi.

Misali a kasar Mozambique karancin ruwan sama ya haddasa fari. Haka a kasa Habasha inda hatta dabbobi sun soma kanjamewa saboda rashin ciyawa lamarin da ya sa ma makiyaya na sayar da dabbobin kan kowane farashi domin su samu kudin abinci. Da saniyar da ake sayarwa $440 , yanzu da kyar a sayeta $17.

A Somalia irin farin da ya auku a shekarar 2011 da ya hallaka mutane 260,000 ya soma kunno kai gashi kuma kasar tana fama da rikicin 'yan ta'adan al-Shabab. Wata mata ma da take da garken shanu da rakumai da awakai tace duk sun mutu saura awakai biyu kawai ko su din ma suna gaf da mutuwa. Haka labarin yake a wurare da dama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG