Mutane 21 Sun Mutu, 23 Sun Bace Bayan Kifewar Kwale-kwale A Gabar Tekun Djibouti

Hadarin Kwale-kwale

‘Yan cirani 21 ne suka mutu, wasu 23 kuma suka bace bayan da wani kwale-kwalen da ke dauke da mutane 77 ya kife a gabar tekun Djibouti, lamarin da shi ne na biyu cikin makonni biyu, kamar yadda hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ranar Talata.

WASHINGTON, D. C. - Mutanen da ke cikin kwale-kwalen sun hada da yara, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) a wani sako da ta wallafa a dandalin sada zumunta na X.

Dubun dubatar bakin haure ne daga yankin kuryar Afirka, musamman daga kasashen Habasha da Somaliya, ke barin nahiyar ta kasar Djibouti, da nufin isa kasar Saudiyya da sauran kasashen yankin Gulf domin samun aikin yi, a cewar hukumar ta IOM.

Da yawa sun gaza, kuma dubbai suna makale a Yemen inda suke rayuwa cikin mawuyacin hali, in ji IOM. Nutsewa a ruwa ya zama ruwan dare a cikin ruwan kasar Djibouti yayin da bakin hauren ke yin balaguro.

Tanja Pacifico, shugaban ofishinsa na Djibouti, ya ce adadin wadanda suka mutu a ranar Talata ya karu daga alkaluman farko na IOM 16.

An kuma ceto wasu mutane 33 daga cikin ruwan, ta kara da cewa su da dukkan wadanda suka mutu ‘yan kasar Habasha ne.

"Abin da ke da ban mamaki shi ne cewa mun samu wani hatsarin jirgin ruwa tare da 'yan kasar Habasha 38 kasa da makonni biyu da suka gabata," in ji Pacifico ta wayar tarho.

-Reuters