Musulunci da Kiristanci Sun Haramta Yin Luadi da Madigo

Musulman Najeriya

Musulman Najeriya

Shugabannin addini Musulunci da na Kiristanci sun goyi bayan dokar hana luadi da madigo da ama auren jinsi daya.
Shugabannin Musulunci na yin nuni da azabar da aka yiwa al'ummar Annabi Lot kamar yadda ya zo a Kur'ani haka ma Kiristoci na nuni da zabar da aka yiwa al'ummar Sodom da Gomara (al'ummar Lot) kamar yadda yake a Littafi Mai Tsarki ko Bible dangane da amincewarsu da dokar hana luadi da madigo.

Ga shugaban kungiyar Izala ta Najeriya Sheik Abdullahi Bala Lau abun da ya faru wata gagarumar nasara ce ga al'ummar dake kiyaye doka da oda ta hanyar cusa mutunta tarbiyar dan adam. Ya ce a shari'ar Musulunci idan an samu mai yin luadi ko madigi ana yi masu zaba mai karfi kamar kashesu ko kuma a turosu daga gini mafi girma domin su fado a yi masu kisan wulakanci. Musulunci na yin hakan domin a nunawa mutane cewa wannan dabi'ar ba abu ba ne mai kyau kuma gani ga wani ya isa tsoron Allah.Duk kasar da ta ce zata yi abun da Allah ya ce kada a yi tamkar tana fito-nafito ne da Allah.

Musulmai sun yaba da dokar da ta tanadi daurin shekara 14 ga duk wanda aka kama. Abun yabawa ne majalisun dokoki da gwamnati suka yi. Matakin kare kasa ne da hanata fadawa cikin fushin Allah. Duk abun da Allah ya haramta kuma kasa tana yi to tana tafe da fuskantar wani bala'i daga wurin Allah.

Shi ma sugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya Pastor Ayo Orisajefor ya yi watsi da duk wata barazana da kasashen dake barin auren jinsi daya bisa hujjar mutunta dokokin bani adama.Pastor Simon Donli shugaban matasan Kiristoci ya ce Allah da kansa ya yi namuji da mace ne. Allah bai shirya aure tsakanin namuji da namuji ba ko mace da mace ba. Ya ce abun dake faruwa shaidanci ne suka sa a gaba. Ya ce dokar da aka yi ta kasarmu ce kuma muna da ikon mu yi hakan. Su kasashen da suke zargin kasarmu su je su yi abun da zasu yi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Musulunci da Kiristanci Sun Haramta Yin Luadi da Madigo - 3:36