Su matasan da suka yiwa yarinyar fyade sun bata kwaya ne wadda ta juya mata hankali kana suka yi mata fyade daya bayan daya. Yarinyar mai suna Aishatu Rabiu yau kwananta tara kwance a asibiti cikin garin Kontagora ba da sanin inda take ba.
Dr Isa Mohammed likitan dake kula da asibitin ya yi bayanin halin da yarinyar ke ciki. Ya ce har yanzu maganin da aka bata da ya sa ta barci har yanzu yana aiki a jikinta. Kawo yanzu bata iya magana yadda ya kamata. Likitan ya ce ba za'a iya sanin irin maganin da suka bata ba sai an yi cikakken bincike.
Malama Hafsat Kassim mai jinyar yarinyar ta kara haske kan lamarin. Ta ce da safe da yamma ana yi mata gyaran gabanta sabili da abun da ya faru. Da farko da aka kawo ta yarinyar ta yi kwana hudu baki a rufe abinci baya wucewa. Yanzu wani zibin jikinta sai ya yi sauki amma idan dare ya yi sai ya tashi. Akwai lokacin da nunfashinta ya tafi. Yanzu dai ana bata magani da yi mata allura da kara mata ruwa a jiki.
Mahaifin yarinyar Malam Muhammed Rabiu ya bayyana takaicinsa a wani yanayi na bacin rai. Matsayinsa yanzu shi ne a nemar ma 'yarsa hakinta. Ya nemi a taimaka masa a ba 'yarsa hakinta tun da shi bashi da wannan karfi sai dai Allah.Ya roki wadanda iko ke hannunsu su taimakeshi. Ya ce adalci ba nuna mutum ya zo ya kashe maka 'ya ba.
Bayanai sun nuna cewa wadanda suka tafka wannan ta'asar sun kai su shida. Amma rundunar 'yansandan jihar Neja ta ce matasa uku ne. Kakakin 'yansandar jihar Mr. Richard Adamu da ya sanarda hakan ya ce tuni har sun cafke daya daga cikin matasan yayin da suka dukufa wacen farautar sauran.
To sai dai lamarin fyade na kara yaduwa a jihar ta Neja lamarin dake bukatar kulawar mahukuntan jihar.
Ga rahoto.