Sai dai wani abun mamaki shine Kotun ta yanke hukuncin yin bulala 20 ne, da kuma biyan diyyan Naira dubu biyar.
Mutumin da aka yankewa hukuncin yace an dade da faruwar lamarin, kuma tursasa masa aka yi.
“Nace masa gaskiya akwai zafi. Bayan wannan ni ban sake yi ba.”
Malam Alhassan Zakariya shine mataimakin darektan hukumar Hizbah a hukumar shari’ar Musulunci ta jihar Bauci.
Yace “bamu da ja da hukuncin da hukumar shari’a ta yanke, saboda dama kotu tana amfani ne da abunda yake gabanta”.
Najeriya dai a baya-bayannan ta sha suka da caccaka daga kasashen yammacin duniya dangane da rattaba hannu da shugaban kasar Goodluck Jonathan yayi, dake hana auren Jinsi daya da luadi.