Monguno Ya Maye Gurbin Ndume A Matsayin Mai Tsawatarwa A Majalisar Dattawa

Sanata Mohammed Tahir Mungono

A yau Laraba, Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da cire Sanata Ali Ndume daga kan mukaminsa .

Sanata Tahir Monguno, mai wakiltar Arewacin Jihar Borno, wanda shine shugaban Kwamitin kula da bangarorin Shari’a, ‘Yancin dan Adam da kuma Dokoki, ya maye gurbin Sanata Ali Ndume , mai wakiltar Kudancin Jihar Borno, a matsayin Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawan Najeriya.

Sanata Mohammed Ali Ndume

Da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya bukaci a kada kuri’a akan batun ta hanyar amfani da murya, mambobin kwamitin kolin jam’iyyar APC a Majalisar Dattawan sun goyi bayan sauke Ndume daga kan kujerarsa.

Hakan na zuwa ne sakamakon sukar baya-bayan nan da Ndumen ya yiwa gwamnatin Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu.

Wata wasika da shugabancin apc na kasa ya aikewa kwamitin kolin jam’iyyar a Majalisar Dattawa, ta bukaci Ndume yayi murabus daga zama mamba a jam’iyyar tare da shiga duk jam’iyyar adawar daya zaba.

Wasikar na dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Sakatarenta Barista Ajibola Basiru.