Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya Ta Fara Takun Saka Da Gwamnati Kan Yarjejeniyar Samoa


Shugaba Bola Tinubu a zagaye da wasu jami'in gwamnatinsa yayin da ya rattaba hanu akan dokar rancen dalibai.
Shugaba Bola Tinubu a zagaye da wasu jami'in gwamnatinsa yayin da ya rattaba hanu akan dokar rancen dalibai.

Majalisar dokokin Tarayyar Najeriya ta ce ba za ta yarda gwamnatin kasar ta shiga wata yarjejeniyar kudi da za ta take dokar kasa ba, biyo bayan tada jijiyar wuya da korafe korafe da aka yi kan rattaba hannu da Najeriya ta yi a wata yarjejeniyar Samoa na kudi dalar Amurka bilyan 150.

Yarjejeniyar hadin gwiwa ce tsakanin Kungiyar Kasashen Turai ta European Union da kuma mambobin kasashen Afirka, Caribbean da Pacific ta OACPS.

Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 28 ga watan Yuni na wannan shekara, amma an fara tattaunawa kan yarjejeniyar ne a shekara 2018 a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73. Kasashen Kungiyar EU 27 da na Kungiyar Kasashen Afirka da Carribean 79 sun rattaba hannu a garin Apia ta kasar SAMOA a ranar 15 ga watan Nuwamba na shekara 2018.

Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya
Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya

Wannan yarjejeniya tana da batutuwa 103 a ciki har da amincewa da masu madigo, luwadi da kuma auren jinsi wanda aka fi sani da LGBTQ.

To sai dai Najeriya ta rattaba hannu ne bayan nazari da tuntubar kwamiti da ma'aikatar kasafin kudi da tsare tsare ta tarayya (FMBEP) da hadin gwiwar ma'aikatar harkokin kasashen waje (MFA) da gwamnatin taraiyya suka yi inda

Ma'aikatar Shari'a ta kasa ta tabbatar da cewa babu daya daga cikin sharuddan 103 da suka saba wa kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ko kuma dokokin Najeriya.

NLC protestors in front of Nigeria National Assembly
NLC protestors in front of Nigeria National Assembly

To sai dai abinda ya dauki hankali shi ne wani rahoto da ya nuna cewa yarjejeniyar tana da wasu sharudda da suka tilasta wa kasashe masu tasowa su goyi bayan al'ummar da ke madigo da luwadi wadanda aka fi sani da lesbian da Gay ko LGBTQ don amincewa da sharadin samun kudi da sauran kayan tallafi daga mambobin kungiyar da suka riga suka cigaba.

Game da ko Majalisar kasa tana da labarin wadannan kudade dalar Amurka biliyan 150, gagarabadan Majalisar Dattawa kuma daya cikin 'ya'yan kwamitin Kasafin Kudi Mohammed Ali Ndume yayi bayani cewa, Majalisa dai ba ta da masaniya kan wadannan kudade, kuma kundin tsarin mulkin kasa ya tanadi cewa dole ne Shugaban kasa ya nemi izini da amincewar Majalisa kafin ya nemi ko wane irin bashi ko na cikin gida ko na kasashen waje. Ndume ya ce in har za a yi maganar samun kudi na taimakawa kasa mai sharadin amincewa da auren jinsi ko masu madigo da luwadi, Majalisa ba za taamince ba.

Sanata Mohammed Ali Ndume
Sanata Mohammed Ali Ndume

A nashi bayanin, Shugaban Kungiyar CISLAC da ke inganta ayyukan Majalisu kuma babban Shugaban Kungiyar Amnesty International a Najeriya Auwal Musa Rafsanjani ya ce, Shugabanin Najeriya na neman a dama da su a hadahadar duniya saboda haka idan akwai wani tallafi ko wani agaji ko rance da za a ba Najeriya da ke da sharuda, za su iya rattaba hannu domin a karbe su a waje. Rafsanjani ya ce ko yaya ne dai, dole ne a yi wa 'yan kasa bayani saboda kar a yi wani abu da zai saba dokokin kasa, domin haka kungiyoyi za su sa ido kan irin wadannan matakai domin kar su ja wa kasar mugun al'kaba'i.

Ita ma Shugabar gidauniyar kula da sha'anin harkokin Mata ta Tozali, Barista Maimuna Yaya Abubakar ta ce a duk lokacin da Najeriya za ta sa hannu a irin wannan yarjejeniya, ta rika lura da sharuddan da ake sawa a ciki, saboda gudun kar a bata wa Najeriya suna. Maimuna ta ce ya kamata a duba tarbiyar yaran mu da addinin mu na kasar da Musulunci da Kiristanci, saboda kar a bata mana al'ada.Ta kara da cewa, gwamnati ta koma ta soke fanin da doka da addini basu yarda ba.

Sai dai gwamnatin tarrayya ta fito da sanarwa dangane da batun inda ta bayyana cewa, babu yadda za a yi ta shiga irin wannan yarjejeniyar. Saboda duk abinda za ta yi, za ta yi shi ne saboda al'umman kasar saboda haka ba za ta yi abinda ya saba wa dokokin kasar ba.

Ofishin kula da basussuka na Najeriya (DMO) ya sanar da cewa, bashin da ake bin kasar ya karu sosai zuwa Naira tiriliyan 121.67 (kimanin dala biliyan 91.46) ya zuwa ranar 31 ga watan Maris. A cewar sanarwar da hukumar ta DMO ta fitar, wannan adadi ya kunshi basussukan cikin gida da waje na gwamnatin tarayyar Najeriya, da gwamnatocin jihohi talatin da shida, da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Saurari cikakken rahoton:

Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya Ta Fara Takun Saka Da Gwamnati Kan Yarjejeniyar Samoa
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG