Bayan doguwar muhawara da aka tafka a zauren Majalisar Dokokin Najeriya, Majalisar Dattawa ta amince da kudirin hukuncin kisa ga masu safarar muggan kwayoyi ko kuma ta’ammali dasu.
Kudirin dai ya samu amincewar rinjayen ‘yan Majalisar ta dattawa, kuma ya tsallake mataki na biyu.
Da farko dai kudirin dokar sashi na 11 karkashin dokar Yaƙi da sha da ta’ammali da kuma safarar muggan kwayoyi, (NDLEA Act) yayi tanadin hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da laifin shigowa, ko safarar muggan kwayoyi ko kuma sarrafa su.
Sai dai yanzu ‘yan Majalisar dattawan sun yiwa wannan sashi kwaskwarima, inda suka mayar da shi hukuncin kisa ga masu aikata irin wannan laifi.
Sanata Tahir Monguno, mai wakiltar Arewacin Jihar Borno, shine shugaban Kwamitin kula da bangarorin Shari’a, ‘Yancin dan Adam da kuma Dokoki, wanda kuma a karkashin kwamitin sa ne aka gabatar da wannan kudiri, duk da cewa da farko kudirin bayyi tanadin hukuncin kisa ga masu aikata irin laifin ba.
Mai tsawatarwa a Majalisar, Sanata Ali Ndume, Sanata me wakiltar Kudancin Jihar Borno, shine ya bijiro da tanadin hukuncin kisa ga duk masu safarar muggan kwayoyi da dangoginsu, wanda daga baya kudirin nasa ya samu amincewar Majalisar.
A hirar ta da Muryar Amurka, Barrister Altine Ibrahim, ɗaya ce daga cikin mata masu fafutukar kare ‘yanci mata da yara, ta ce “wannan kudiri doka yazo ne akan gaɓa, ganin cewa yadda yara da mata suka faɗa harkar shaye-shayen muggan kwayoyi”
‘Yan Najeriya dai na fatan fara ganin irin waɗannan hukunce-hukuncen a zahiri, kamar yadda suke a rubuce.
Saurari cikakken rahoto daga Ruƙaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna