Majalisar Dokokin Najeriya ta kara wa'adin aiwatar da kasafin kudin shekara 2023 zuwa karshen watan Disamba na wannan Shekara,
Wanan mataki da Majalisar ta dauka ya biyo bayan wata wasika ne da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiko wa Majalisar inda ya bukaci a kara wa'adin aiwatar da kasafin kudi na Naira triliyan 21.83 na shekara 2023 wanda gwamnatin Tinubun ya gada daga gwamnatin da ta gabata.
Za a hada har da wata kwaryakwaryar kasafi na triliyan 2.17 wanda Tinubu ya kawo bayan ya karbi mulki da wattani 6. Shi ne ya kawo jimlar kasafin kudin zuwa Naira triliyan 25.
Sanata Mai Waklitan Jihar Borno ta Kudu kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin kula da kasafin kudi a Majalisar Datawa Mohammed Ali Ndume yayi wa Muryar Amurka bayanin hujjar da ya sa Majalisa ta dauki wannan matakin.
Yace akwai wasu manya manyan aiyuka da ba a yi su ba kuma shekarar ta kare har an shiga 2024, shi ya sa aka kara wa'aidin aiwatar da kasafin kudin na bara.
Ya kara da cewa Majalisa ba ta kara ko anini akan wannan Kasafin.
Sanatan ya kuma ce ba a fara amfani da kasafin kudin bana ba, amma za a bi aiyukan daki daki tare da bin umurnin hanyoyin aiwatar da kasafin daga karshen watan bakwai.
Sai dai kwararre a fanin tattalin arziki, Yusha'u Aliyu ya ce shi bai yi mamakin halin da aka shiga wajen aiwatar da kasafin kudin bara ba saboda tun lokacin da Shugaban Kasa ya kaiwa Majalisa kwaryakwaryar kasafin kudi na triliyan 2.17 a watan Nuwamba, an makara, domin a wannan lokaci ana batun yin sabon kasafi ne.
Saboda haka bai kamata a rika bari ana yin haka a daidai lokacin da ya kamata a ce an riga an aiwatar da kasafin shekara kusan kashi 80 cikin dari ba, kn ba haka ba, zai kawo rudani har ba za a san wanne za a kashe ba, kamar yada aka samu yanzu.
Yusha'u ya ce wayar da kan mahukunta akan tsarin kasafin kudi da yadda za a rika aiwatar da shi yana da amfani kwarai da gaske.
Majalisar ta kwashi sa'o'i hudu tana wannan aiki, bayan ta yi zaman sirri na awanni biyu.
Wannan shi ne karon farko da Majalisa za ta kara wa'adin aiwatar da wani kasafin kudi har sau uku.
A baya ta kara daga watan Janairu zuwa watan Maris na bana, sannan kuma aka kara wa'adin zuwa wannan watan na Yuni.
A saurari rahoton Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna