Wannan dai shi ne kudurin shugabannin Majalisun biyu, ta Dattawa da Wakilai bayan sakamakon bayanan shari'ar da kotun koli ta bayar a Abuja.
Senator Godswill Akpabio shugaban Majalisar Dattawa ya ce Kotun koli ta zartas da hukunci, ya kuma rage wa majalisun su tabbatar da cin gashin kan kananan hukumomin bisa tsarin doka da ta ba kowane bangare hurumin sa.
Shi kuwa kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas cewa ya yi gaskiya ta zama dokin karfe a nasarar samowa kananan hukumomi ‘yancin tsayuwa kan kafafunsu, domin daga yanzu kuwa aiki ne tukuru ake sa ran kananan hukumomi su fara yiwa jama'arsu don chin moriyar romon Dimokradiyya.
Shugabannin sun ja kunnuwan Gwamnonin jahohi da su tabbatar da bin umarnin kotun kolin bisa tafarkin tsarin mulki da ya kebewa kowane bangare hurumin sa, wato Gwamnatin taraiyya da jahohi da kuma kananan hukumomi.
‘Dan majalisa daga jihar Bauchi Auwalu Abdu Gwalabe dai ya yi tsokaci cewa yanzu ne za a ga aiki da cikawa domin shugabanin kananan hukumomi za su yi karfi sosai wajen gudanar da shugabanci, amma fa su sani cewa idan sun yi almundahana to fa kansaloli suna da hurumin tsige su.
Shi ma Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu Ali Ndume ya jaddada cewa a yanzu dai ya ragewa Gwamnonin jahohi su tabbatar da nasarar karfafa gwiwa da aka yiwa kananan hukumomin domin yin wani abu da ya sha bamban da hakan, na da sakamakon sa.
Ndume ya ce dole ne al'umma su sa ido a yadda shugabanin kanana hukumomin za su rika yin aiki,saboda a hana yin sama da fadi da kudaden da za a ba su kai tsaye.
Manazarta na ganin wannan hukunci zai magance kashi 90 cikin dari na matsalolin da ake fama da su a kasar a cikin ‘dan kankanin lokaci.
Saurari cikakken rahot daga Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna