Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na ci gaba da gudanar da bincike kan wani harin da ‘yan bindiga suka kai wani babban shagon sayar da kayayyaki mai cike da hada-hada da ke yankin Karu dab da Abuja.
A farkon wannan makon ne dai wasu gungun ‘yan bindiga suka kai hari da bindigogi a kan wani babban shago a Mararraba da ke yankin Karamar Hukumar Karun jihar Nassarawa da ke dab da Abuja.
Wannan harin dai ya yi matukar tada hankalin mazauna wannan yankin da ke da yawan jama’a da zirga-zirgar ababen hawa.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Nasarawa, DSP Rahman Nansel, ya tabbatar wa Muryar Amurka cewa, mutum hudu ne suka rasa ransu bayan da ‘yan bindigar suka bude wuta jim kadan bayan sun mamaye shagon.
A cewar kakakin ‘yan sandan, bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sanda ya aike da wasu zaratan jami'ansa, inda suka taras da mutane hudun da aka harba cikin jini malala.
Bayan da aka kai su asibiti ne kuma likita ya tabbatar da dukkanninsu rai ya yi halinsa, wato sun riga mu gidan gaskiya.
Masanin tsaro Dakta Yahuza Getso ya ce galibi dai ire-iren wadannan hare-hare na faruwa ne a watannin ukun karshen shekara, amma wannan ya zama sabon abu da ba’a saba ganin ya faru a watan farko na sabuwar shekara ba.
Abin da hakan ke nufi, in ji Dakta Getso, shi ne rauni irin na jami'an tsaro, kasancewar yankin cike yake da jama'a da ababen hawa, amma har azo a tafka irin wannan ta'asa ba tare da an cafke miyagun ba.
A gefe guda kuma, ‘yan sandan jihar Nasarawa na kara neman goyon bayan jama'a kamar yadda suka ce, su kadai baza su iya shawo kan kalubalen tsaro ba, dole sai ana yi ana ba su bayanan sirri.
Jihar Nassarawa dai na daya daga cikin jihohin tsakiyar Najeriya da ke fama da kalubalen tsaro iri-iri, domin a baya ma an taba sace tsohon mataimakin gwamnan jihar, an kuma sace wasu daliban jami'ar tarayya da ke babban birnin jihar.
A garuruwan jihar da ke dab da Abuja, an taba sace wasu daliban firamare, an sace shugaban karamar hukumar Keffi, sannan a farkon wannan makon an sace shugaban karamar hukumar Akwanga, a kuma wannan rana ne aka kai hari kan wannan babban shago.
Jami’an tsaro a Najeriya dai na cewa suna iya bakin kokarin su domin shawo kan matsalar tsaro a sassa daban-daban na kasar, kokarin da masana tsaro ke cewa bai isa ba.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5