Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Arangama Tsakanin 'Yan banga Da 'Yan Bindiga Ta Yi Sanadin Mutuwar Gomman Mutane A Taraba


Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba (Faceboo/Gwamnatin Taraba)
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba (Faceboo/Gwamnatin Taraba)

Arangama tsakanin jami’an banga da 'yan bindiga ta haifar da asarar rayuka sama da 70 a garin Tiggi da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin ta SP Usman Abdullahi Jada, wanda ya kara da cewa yanzu haka an dawo da doka da oda a yankin da abin ya faru.

Da yake zantawa da Sashen Hausa, kwamandan 'yan bangar Tiggi ya ce sun kashe 'yan bindiga sama da talatin, amma su ma sun sami asarar jami’ansu 15.

Shugaban kwamitin samar da zaman lafiya na yankin Bali da Gasol, Zubairu Sajo, ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta kai musu agajin gaggawa a yankin baki daya.

Ardo Tim Tim wanda ya yi rashin 'yan uwa sakamakon wannan hari ya nuna rashiN jin dadinsa sakamakon ga asarar rayuka da suka yi, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su kai musu dauki.

Domin Karin bayani saurari rahotan Lado Salisu Garba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG