Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Munanan Hare-Haren ‘Yan Ta’adda A Jihar Filato


Shugaban Kasar Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya, Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa, tare da hada karfi da karfe domin zakulo duk wadanda suka aikata wannan mummunan hari da tabbatar da kamo masu hannu a ciki.

Shugaba Bola Tinubu, yayi Allah-wadai dangane da mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai jihar Filato wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi.

Shugaban ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Cif Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya fitar a yau ranar 26 ga Disamba, 2023.

Shugaba Tinubu ya bayyana kakkausar suka dangane da munanan hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Filato, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 160 kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ta ruwaito.

Sai dai Rundunar 'Yan Sanda a jihar Filato ta ce mutane 96 ne aka hallaka a hare-haren.

An kai hare-haren ne a daren jajibir na Kirsimeti 24 ga watan Disamba da kuma washegari ranar Kirsimeti, inda ‘yan bindiga suka mamaye kauyuka da dama a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Bayaga mutane da suka rasa rayukansu, akwai kuma daruruwa wadanda suka jikkata wadanda ake kula da su a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos da kuma asibitin gwamnati da ke Barikin Ladi.

Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa, tare da hada karfi da karfe domin zakulo duk wadanda suka aikata wannan mummunan hari da tabbatar da kamo masu hannu a ciki.

Shugaba Tinubu ya jaddada bada agajin gaggawa ga duk wadanda abin ya shafa tare da tabbatar da kula da lafiyar wadanda suka jikkata.

Da yake jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Filato, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tabbas gwamnati baza ta bar wadanda suka kai harin su tsira ba kuma za’a dauki tsauraran matakai akan haka.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, a wata hira da gidan talabijin na Channels wato Channels Television a turance, ya bayyana hare-haren a matsayin "hari na rashin hankali" tare da bayyana mummunar illar da harin yayi ga al'ummomin da a lokacin ke shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti cikin lumana.

Bugu da kari, Gwamnan yayi alwashin bin kadin lamarin tare da tabbatar da kwato haqqin wadanda abin ya shafa wajen tabbatar musu da adalci.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG