Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta shirya tsaf domin ganin cewa an gudanar da zaben gwamnoni da za’a sake gudanarwa a jahohin biyu na Abiya da Imo, a sakamakon matsalolin da aka fuskanta a zaben da ya gabata.
Babban jami’in ‘yan sanda mai kula da shiyya ta tara kuma mai mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya AIG Usman A Gwari a hirar su da Lamido Abubakar Sokoto ya bada tabbacin cewar a shirye suke domin tabbatar da tsaro dakuma bin doka da oda a wadan nan wurare.
Jami’in tsaron yayi Karin bayani kamar haka “rundunar ‘yan sanda ta shirya domin gudanar da wannan zabe da za ayi gobe asabar a wasu kananan hukumomin wadan nan jahohi guda 9, kuma akwai isassun jami’an tsaron da suka hada da ‘yan sanda, sojoji, civil defens da sojojin ruwa da sauran su”.
Zabe a wadannan kana nan hukumomin y azo da matsala ne yayin da aka sami sace sacen na’urar tantance katunan zaben da kuma akwatunan zaben wanda hakan ya haifar da rudani a wasu yankunan jahohin kuma yayi sanadiyyar soke zaben.
Hukumar zaben jahar Abiya ta ce tariga ta rarraba kayan aiki a sassa daban daban haka ita ma takwarar ta ta jahar imo tace ta riga ta kammala raba wadan nan kayan aiki.
Your browser doesn’t support HTML5