A kokarin kawar da cutar shan inna wadda aka fi sani da polio daga doron kasa da kungiyar lafiya ta duniya wato WHO ke yi, Yau ce ranar farko ta makon yin allurar riga kafin cututtuka a Najeriya.
A jahar Naija, ranar Asabar ne za’a fara aikin bada rigakafin cutar shan inna karo na uku a wannan shekarar. Jami’an lafiya a jahar bsun ce sun kammala duk wasu shirye shirye da suka wajaba na tabbatar da yin aikin cikin nasara.
Mustapha Nasiru Batsari ya zanta da daraktan sashin kula da riga kafin na jahar Naija Dr Yabagi inda yayi kain bayani n cewa “na farko dai mun yi kokarin sanin adadin yaran da za’a ba wannan magunguna kuma zamu bi gida gida kamar yadda muka saba domin bada wannan magani”.
Jami’an lafiya a fadin jahar gabaki daya sunyi kira ga jama’a domin bada goyon bayan su wajan bari a diga wa yaran su wannan magani. Alhaji baba duku, jami’in hulda da jama’a na ma’ai katar lafiya ta jahar Naija, yayi Karin bayanin cewar “iyaye sun saba bamu hadin kai dan haka ina kira garesu da su taimaka su bar ma’aikatan mu su shiga gidajen su domin bada maganin”.
Cutar shan inna ko Polio na da illa ga kananan yara yayin da take gurguntar da su musamman saboda rashin karbar rigakafin cutar, kuma kungiyar lafiya ta duniya na yin iya bakin kokarinta wajhan ganin kawo karshen wannan cuta a duniya.