Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JIHAR NEJA: Sabon Gwamna Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki


Gwamnan jihar Neja mai barin gado tare da Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa yayinda suk cikin PDP
Gwamnan jihar Neja mai barin gado tare da Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa yayinda suk cikin PDP

A jihar Neja sabon gwamna mai jiran gado ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki da gwamnatin Muazu Babangida akan mika mulki ranar 29 ga watam Mayu.

Sabon gwamnan jihar Neja mai jiran gado Alhaji Abubakar Sani Bello ya kaddamar da kwamitin da zai yi aikin karbar mulki daga gwamnatin Babangida Aliyu mai barin gado.

Kwamitin da mataimakin sabon gwamnan Alhaji Muhammad KO ke jagoranta zai yi aikin tantance duk takardun bayanan gwamnati ne dalla dalla kamar yadda sabon gwamnan ya bayyana.

Sabon gwamnan yace kwamitin da ya kafa zai zauna da na bangaren gwamnati ya duba abubuwan dake kasa a kowace ma'aikatar gwamnati da halin da gwamnati ke ciki domin su tacesu. Bayan tacewa zasu samu hasken yadda zasu fara tasu gwamnatin.

Dangane da ko akwai inda ba zasu gamsu ba, sabon gwamnan yace ya gayawa 'yan kwamitin duk abun da basu gane ba su yi tambayoyi domin a basu cikakken bayani. Sabon gwamnan ya tabbatarwa mutanen Neja yin adalci.

Shi ma gwamna mai barin gado Muazu Babangida Aliyu ya kafa kwamitin mika mulki ga sabuwar gwamnati a karkashin shugabancin sakataren gwamnatin jihar Alhaji Idris Ndako wanda ya bayayana irin ayukan da zasu gudanar. Yace gwamnan jihar ya umurcesu su saka duk kudaden da ya samu tun daga lokacin da ya karbi mulki a rahotonsu tare da bayani akan ayyukan da ya yi da wadanda ya fara amma bai gamasu ba.

Dangane da ko suna da wata fargaba ganin cewa ba PDP ba ce zata cigaba da mulki Alhaji Ndako yace basu da wata fargaba. Yace an riga an gama aikin jam'iyya yanzu aikin gwamnati aka shiga.

Akan rade-radin da ake yi cewa wasu mukarraban gwamnatin jihar sun riga sun yi ta kare sai Alhaji Ndako yace idan akwai wadanda zasu gudu sai shi da gwamna Babangida kuma suna nan basu je koina ba.

Sakataren gwamnatin jihar yace tuni suka yiwa sabon gwamnan tanadin inda zai zauna na wucin gadi. Yace sun bashi masaukin shugaban kasa dake harabar gidan gwamnati. Sabon gwamnan ya shiga cikin gidan ya fara aiki kafin a rantsar dashi ranar 29 ga watan Mayu.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG