A jawabin da ya gabatar, Volker Turk ya yi Allawadai da yadda ake tauye hakkokin masu neman kaura da ‘yan gudun hijra a fadin kasar Libya, abinda ya haifar da wata hanya mai tsananin hatsari da ta ratsa hamadar Sahara ta tike zuwa yankin kudancin tekun maditariniyan.
A cewar Turk, gwamnati da kungiyoyi na cigaba da cin karensu babu babbaka wajen tauye hakkokin masu neman kaura a wani irin mataki mai girma, inda laifuffukan da ya zayyana ana aikatawa suka hada da safarar bil adama da azabtarwa da bautarwa da tatsar kudade da yunwa da dauri da kuma korar dimbin jama’a a lokaci guda.
A jawabin da ya gabatar a birnin Geneva game da tarihin tauye hakkokin bil adama a kasar Libya a shekaru 10 da suka wuce, Turk ya shaidawa kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya cewar, “ina umartar hukumomin kasar da su gaggauta yin martani game da bincikenmu, tare da gudanar da cikakken bincike akan wadannan laifuffuka.”
Bai bada karin haske akan bayanan gawawwakin dake cikin makeken kabarin ba ko kuma yadda aka samar da shi.
Mai magana da yawun ofishin Turk yace, “bamu samu wani bayani daga hukumomi ba amma muna ci gaba da bibiya.
-Reuters