Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Haure Akalla 107 Aka Kubutar Daga Azaba A Kudu Maso Gabashin Libya


Bakin Haure
Bakin Haure

Bakin haure akalla 107 da suka hada da mata da yara da ke garkame ne aka kubutar a wani gari da ke kudu maso gabashin kasar Libya, kamar yadda wani mai magana da yawun hukumar tsaron kasar ya sanar a ranar Litinin.

WASHINGTON, D. C. - Walid Alorafi, mai magana da yawun hukumar binciken manyan laifuka (CID) a Benghazi, ya ce wasu bakin haure sun ce, an tsare su har na tsawon watanni bakwai kuma "sun so su tafi Turai ne."

Alorafi ya ce bakin hauren sun fito ne daga kasashe daban-daban na kudu da hamadar Sahara amma akasari daga Somalia.

“Mun kai samame a wata maboya da ke cikin garin Kufra a daren jiya, kuma mun gano bakin haure da suka hada da mata da yara da kuma tsofaffi wadanda wasu ke da alamun azabtarwa da harsasai a jikinsu,” in ji Alorafi.

Alorafi ya kara da cewa "An mika dukkan bakin hauren ga hukumar kula da shige da fice ta haramtacciyar hanya domin kammala musu wasu hanyoyin."

“Wasu daga cikin bakin haure ba su da koshin lafiya sosai,” in ji Alorafi.

Kufra dai na da tazarar kilomita 1,712 (mil 1,064) daga Tripoli babban birnin kasar.

Kuma Libya ta zama wata hanyar safarar bakin haure ne da ke tsere wa rikici da fatara zuwa Turai ta hanyar mai hatsari da suke bi ta hamada da kuma tekun Bahar Rum tun bayan hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a wani boren da kungiyar tsaro ta NATO ke mara wa baya a shekara ta 2011.

Tattalin kasar na arzikinta man fetur kuma ya zama abin jan hankali ga bakin haure masu neman aiki.

Libya mai arzikin man fetur na da bakin haure 704,369 daga kasashe sama da 43, a cewar bayanan da aka tattara a kananan hukumomi 100 na Libya a tsakiyar shekarar 2023, alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna haka.

A cikin watan Maris, Hukumar Kula da Hijira ta Duniya ta ce ta hanyar CID an gano akalla gawarwakin wasu bakin haure 65 a wani kabari da ke kudu maso yammacin Libya.

"Ina kira da a karfafa hadin gwiwa a yankin don tabbatar da tsaron bakin haure," in ji manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya Abdullah Bathily a jawabinsa ga kwamitin sulhu a watan Afrilu.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG