A karshen makon jiya ne babban kwamandan rundunar mayakan Nijar Janar Salifou Modi ya yi rangadi a Bamako, inda suka tattauna da hukumomin Mali a ci gaba da neman hanyoyin murkushe matsalolin ta’addancin da suka addabi kasashen Sahel.
A hirar shi da Muryar Amurka, mai fashin baki kan harkokin tsaro, Seidik Abba, ya ce wannan wani babban ci gaba ne a kokarin dinke barakar da ta maida hannun agogo baya a wannan yaki.
Ya ce rarrabuwar kawunan da aka fuskanta a tsakanin kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso abu ne da ke kara bai wa ‘yan ta’adda kwarin gwiwar ci gaba da yin aika-aika a yankin da ya hada iyaka da kasashe uku.
Ya zama wajibi hukumomin kasashen Sahel su kauda dukkan wasu bambance-bambance a tsakaninsu domin tunkarar wannan matsala da ke barazanar yaduwa zuwa kasashen Togo da Benin, wanda kuma idan ba a yi hattara ba abin na iya shafar nahiyar Afirka baki daya, a cewar Abba.
Ya kara da cewa a can baya dakarun kasashen nan 3 na da ‘yancin su tsallaka kasashen don bin sawun ‘yan bindiga har zuwa kilomita 50 a karkashin yarjejeniyar kungiyar G5 Sahel, to amma rashin jituwa a tsakaninsu ta sa an dakatar da wannan tsari.
Da yake tsokaci kan ziyarar da Janar Salifou Modi ya kai zuwa kasar Mali, Seidik Abba ya ce abu ne mai kyau, kuma a ganinsa ya kamata nan ba da jimawa ba takwaran aikinsa na Mali shi ma ya ziyarci Nijar. Kuma ya kamata lokaci zuwa lokaci kasashen 3 masu fama da tashin hankali su rinka zama don bitar halin da ake ciki.
Saurari hirar Seidik Abba Da Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5