Sanarwar da ma’akaitar tsaron kasar Nijar ta fitar da yammacin ranar asabar, na cewa wani ayarin motocin dakarun tsaro na rundunar Alamahaou da ke sintirin a gundumar Banibangou sun fada tarkon wasu ‘yan bindiga da suka yi kwanton bauna a kewayen kauyen INTAGAMEY iyakar Nijer da Mali.
Bayan shafe lokaci mai tsawo ana barin wuta maharan sun gudu sakamakon yadda sojojin kasa da hadin guiwar sojan sama suka fatatake su.
Sanarwar ta kara da cewa ‘yan bindigar sun tsallaka wata makwaciyar kasa da ba a bayyana sunanta ba. Sanarwar ta na nuni da cewa sojojin 10 ne suka rasa rayukansu, sanadiyar wannan al’amari yayin da wasu 16 suka yi batan dabo sannan wasu 13 suka jikkata, haka kuma an kona motoci 3 inji sanarwar ma’aikatar tsaro wace ta kara da cewa kawo yanzu ba a tantance adadin ‘yan ta’adda da suka mutu ba, amma an tabbatar da cewa sun kwashe wasu gawarwakinsu.
Wani mazaunin gundumar Banibangou da wakilin Muryar Amurka ya tuntuba ta waya, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya bayyana cewa ayarin wasu motoci 10 dauke da sojojin sun fada tarkon ‘yan ta’addan da suka yi masu zobe a wejen kauyen Tiloa inda aka fafata sosai kafin maharan su arce.
A cewarsa, mota daya dauke da wasu sojojin da suka tsira daga harin sun isa kauyen ADABDAB da yammacin juma’a, haka kuma an ga wasu sojoji kimanin bakwai da suka isa wannan gari a kafa wadanda ake kyautata zaton motocinsu ne suka kone kurmus sakamakon barin wutar da aka yi.
Haka kuma ya kara da cewa bayanan da ke fitowa daga bakin jama’ar wannan karkara na cewa ayarin motocin jami’an tsaron a kalla 10, an hango suna sintiri kafin wannan tsautsayi ya afka masu.
Harin na ranar juma’a 10 ga watan Fabarairu 2023 na wakana ne a wani lokacin da aka lura da wasu alamomi dake nunin kura ta lafa a jihar Tilabery, wacce al’ummarta ke ci gaba da dandana kuda sanadiyar lalacewar sha’anin tsaro a kasashen Mali da Burkina Faso.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.