Biyo bayan rikicin da ya barke a Ibi wanda yayi sanadiyar asarar rayuka mukaddashin gwamnan jihar ya kai ziyara yankin domin ya gani da idanunsa irin barnar da aka yi.
WASHINGTON, DC —
A wani yunkuri na tabbatar da dorewar zaman lafiya mukaddashin gwamnan jihar Taraba Alhaji Garba Umaru ya kai ziyarar gani da ido yankin Ibi da yayi fama da rikici kwana kwanan nan.
Yayin ziyarar mukaddashin gwamnan jihar Taraba Alhaji Garba Umaru ya bayyanawa sarakunan yankin Ibi da kuma shugabannin Wukari cewa gwamnatin jihar ba zata bari irin wannan asarar rayuka na faruwa ba a jihar.
A fadar sarkin Ibi mukaddashin gwamnan ya danganta tashe-tashen hankulan da rashin aikin yi. Domin haka ya jaddada aniyar gwamnati da samarma matasa ayyukan yi su samu abun da zasu dogara akai. Yace matasan da suke tada hankali wasu cikinsu na shan kwaya domin basu da abun yi. Yace bayan abun da karamar hukuma zata yi gwamnatin jihar a watan gobe zata sake daukan matasa ta koya masu sana'a. Amma gwamnati ta soke zancen ba matasa babur ko keke-napep. Maimakon haka, gwamnati zata koya masu sana'a kana ta basu jari su fara sana'o'insu.
A nashi jawabin sarkin Ibi Alhaji Abubakar Salihu Bawuro ya sha alwashin cewa ba za'a sake samun irin rikicin da ya faru a yankinsa ba. Yace jukunawan masarautarsa musulmai da kiristoci sun yi taro sun rantse su basu da hannu a rikicin da ya faru kuma ba zasu yadda wani daga cikinsu ya tada hankali ba. Haka ma al'ummar kabilar Tiv duk sun dawo suna rokon gwamnati ta taimaka masu yadda zasu koma kauyukansu da aka kone domin damina ta zo su samu su yi noma. Sun amince Allah ne Ya sa hakan ya faru kuma babu wani da zai dauki fansa akan abun da ya faru. Haka ma Fulani suna rokon su koma aikin kiwo da suke yi ba tare da wani tashin hankali ba tsakaninsu da kabilar Tiv ko Jukun.
A Wukari kuma sarkin garin wato Aku Uka Dr Shekarau Angyu ya bukaci gwamnatin jihar da ta taimaka domin wadanda suka bar garuruwansu da gidajensu su dawo. Ya roki gwamnatin ta daga dokar hana fita na ba dare ba rana da aka kafa ma yankin domin wai mutane suna zagayawa suna sace-sace.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5