A wani taron manema labaran da suka kira a Damaturu, babban birnin jihar, al'ummar na Yobe sun ce wannan doka ta takura ma rayuwarsu matuka.
Shugaban Kungiyar Muryar Talaka a Jihar Yobe, Saleh Bakros, wanda ya jagoranci taron manema labaran, yace su na kira da babbar murya ga shugaba Goodluck Jonathan a kan kada ya sabunta wannan doka a kan jihohin nan uku na arewa maso gabas, tun da dai kafa ta har sau biyu ta kasa magance matsalar tsaro a yankin.
Yace da wannan doka zata iya kawo karshen fitinar da ake fama da ita, to da tuni an ga alamun hakan.
Wani mazaunin garin Damaturu, Mohammed Abdullahi, yace kara sabunta dokar-ta-bacin nan illa ce ga al'umma domin babu abinda kafa ta ya haifar in ban da karin fitina, yana mia misali da yadda al'ummar yankin Gujba suke ta kaura daga gidajensu da garuruwa da kauyukansu zuwa wasu wuraren.
Mallam Ishaku Isa, shi ma mazaunin garin Damaturu, yayi bayanin cewa a kan shiga yanayin dokar-ta-baci na karamin lokaci ne domin a samu sukunin h=shawo kan wata matsala, domin a karkashinta ana daukewa jama'a wasu hakkokinsu na walwala. Yace kafa dokar a karo na farko da na biyu bai biya bukata ba, don haka bai kamata a yi na uku ba tun da babu wata alamar cewa yin hakan zai canja zani.