Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross dake taimakawa mutanen garin na Wukari, Mr. Lucky Abio, yace mutane su na cikin matukar bukatar abinci da ruwa da kuma magunguna a saboda ba su da sukunin fita waje domin sayen wadannan abubuwa.
Yace a saboda babu kowa a waje, wasu bata-gari su na fasa kantunan mutane su na musu sata, don haka yana da kyau a kyale mutane su samu zarafin fita ko da na gajeren lokaci ne domin su samo abinci da kayan bukatu.
Shi kansa mukaddashin gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Garba Umar, ya bayyana cewa bai ji dadin abinda ya gani ba a lokacin da shi da manyan jami'an gwamnatinsa da na tsaro suka ziyarci garin na Wukari.
Mukaddashin gwamnan ya jajanta wa mutanen na Wukari bisa abinda ya faru, yana mai cewa gwamnati zata kara kaimin samarwa da matasa aikin yi domin rage irin wannan rikicin.
Aku Uka na Wukari, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Taraba, Dr. Shekarau Angyu, ya bayyana takaicin wannan rikici na Wukari, sannan ya roki gwamnati da ta sassauto da dokar hana fita da aka kafa.
Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta ce mutane 21 ne aka kashe a wannan rikici, yayin da aka kama 24.