Abin Da Masana Ke Cewa Kan Raba Ma'aikatu Ga Ministoci A Najeriya

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Masanin kimiyyar siyasa na jami'ar Abuja Dr. Farouk B.B Farouk, ya ce korafin wata jiha ta samu karami ko babban Minista ya sabawa tsarin dimokradiyya.

ABUJA, NIGERIA - Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da korafi ke fitowa na wasu jihohin cewa ba su samu ma'aikatu masu gwabi ba.

Dr. B.B Farouk ya ce hurumin Shugaban kasa ne ya nada wanda ya ga ya dace don zama Minista da tura shi ma'aikatar da ya ke son ya yi masa wakilici a cikin ta.

A nan masanin ya nuna tamkar masu muhawarar ba sa la'akkari da tsarin Shugaba mai cikakken iko ne da Najeriya ke aiki da shi.

Da ya juya kan samun ma'aikata mai tsoka, Dr. Farouk ya ce son samu duk wanda a ka nada ya yi wa kasa gaba daya aiki ne kuma a baya an samu misalan da ke nuna ba lalle hakan ya kan kawo wata riba ba ce.

Ana sa martanin mai bai wa Shugaban kasa shawara kan siyasa Ibrahim Kabir Masari ya bukaci jama’a da su bai wa sabuwar gwamnatin lokaci don ganin sauyin da suka yi alkawari.

A yanzu dai a na jiran sunan Minista daga Kaduna da zai maye gurbin Nasiru Damu El-rufai, sai kuma sakamakon binciken tsaro ga Sanata Sani Abubakar Danladi daga Taraba da Stella Okotete daga Delta.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Da Masana Ke Cewa Kan Raba Ma'aikatu Ga Ministoci A Najeriya.mp3