Batun ko Gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai yana da koshin lafiyar da zai iya komawa kan mulki shi ne ya mamaye siyasar jihar Taraba, inda bangaren gwamnan ke karyata wani bidiyo dake nuna gwamnan jihar na cewa bashi da koshin lafiyar da zai koma mulki.
WASHINGTON, DC —
A cikin wani bidiyo da ya bayyana a shafin internet na Youtube, an ga gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai na bayyana cewa bashi da koshin lafiyar da zai koma kan mukaminsa.
A bidiyon, a ga Danbaba Suntai yana turanci, wanda idan aka fassara yake cewa “Ina samun sauki sosai, amma ka san gaskiya, ba zan ce maka na warke ba da har zan koma in kama aiki, don kawai ina so ka goyi bayana, ganin irin halin da nake ciki yanzu. Ina shawartar jama’a da mu komawa Allah a dukkanin abubuwan da muke yi, mu kuma nisanci shan kayan barasa.”
To sai dai kuma, tuni mukarraban gwamnan suka fitar da wata sanarwa ta hannun tsohon kwamishinnan shari’a na jihar, da ‘yan bangaren Danbaban ke dauka a matsayin sakataren gwamnatinsu. Barrister Timothi Kataf, yace ba haka zancen yake ba.
“An ce shi (Suntai) ba zai iya aiki ba, sai aka sa har Sahara Reporters, har duniya su yarda. A ina gaskiya a cikin wannan. In basu yarda da sauran bidiyo ba, meyasa zasu yarda da wannan yanzu”, in ji Barrister Kataf.
Suma ‘yan majalisar jihar Taraba sun mayarda martani akan wannan sabuwar dambarwa, inda suke cewa suna nan daram, a matakin da suka dauka na cewa gwamnan ya koma ya cigaba da yin Jinya, shi kuwa mataimakinsa Garba Umar ya cigaba da riko a matsayin mukaddashi.
Danbaba Suntai yayi hatsarin jirgi ne a shekara ta 2012 lamarin da ya kaishi doguwar jinya a Jamus da Amurka. A cikin kwanakinnan, wasu na kusa da shi sunyi ta kokarin mayar da shi kan mukaminsa.

Your browser doesn’t support HTML5