Wani rahoton gidan talabijin din CNN da aka wallafa wannan watan ya gano cewa Korea ta Arewa ta sanya hannu kan wasu kwangiloli na miliyoyin daloli a Mozambique.
Bayanai sun yi nuni da cewa Korea ta Arewan ta yi amfani da ribar da ta samu daga sana’ar kamun kifi a gabar tekun Mozambique wajen tafiyar da shirin makaman Nukiliyarta.
Amma mataimakiyar Ministar harkokin wajen Mozambique, Maria Manuela Lucas, ta musanta zargin cewa gwamnatin Mozambique ta yi wata yarjejeniya da Koriya ta arewa wadda ta sabawa takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.
Ta kuma ce kasar na maraba da duk wasu masu ido da za su kai ziyara kasar domin tantance gaskiyar lamarin.
Ms. Lucas ta ce kwanan nan gwamnatin Mozambique ta gayyaci kwamitin Majalisar Dinkin Duniya zuwa Mozambique don ganin ayyukan da kasar ke yi da nufin hada kai da akwamitin.