Gwamnatin Sudan ta Kudu ta janye jakadanta na Amurka, bayan da shugaban Amurka din, Donald Trump ya saka wani takunkumin hana sayar da makamai akan gwamnatin kasar a makon da ya gabata.
Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu na farko, Tabang Deng Gai, ya ce, matakin da Amurkan ta dauka zai kawo cikas wajen yunkurin da ake yi na samar da zaman lafiya a kasar.
Gai ya kara da cewa, takunkumin ya zo musu da mamaki, ganin cewa yana zuwa ne a daidai lokacin da wata tawagar gwamnati ke shirin barin Birnin Addis Ababa domin halartar wani babban taro a karo na biyu, wanda zai dubi yadda za a farfado da yarjejeniyar sulhun da aka cimma a shekarar 2015.
Bangarorin da ke fada a kasar ta Sudan ta Kudu, sun rattaba hanu akan yarjejeniyar dakatar da fadan a karshen taron da suka gudanar a karon farko a watan Disamba.
Sai dai wannan yarjejeniya ta samu cikas, cikin ‘yan kwanakin da suka biyo baya, inda dukkan bangarorin biyu suka saba yarjejeniyar.
Facebook Forum