Kasar Maldives, wacce tsibiri ce, ta abka cikin dambarwar siyasa.
Gwamnati ta gargadi cibiyoyinta da su yi biris da duk wani kira daga kotun kolin kasar, na tsige Shugaban kasar Abdullah Yameen.
“Duk wani umurni daga kotun koli na kama Shugaban kasa zai kasance mai saba ma kundin tsarin mulkin kasa kuma mara hurumi,” a cewar Attoni-Janar din shari’ar kasar Mohammed Anil a yau dinnan Lahadi a wani jawabinsa da aka yada a gidan talabijin din kasar.
A makon jiya kotun kolin ta bayar da umurnin sakin wasu ‘yan adawar siyasa su 9 da kuma wasu ‘yan majalisar dokoki 12 da ke adawa da Shugaban kasar, ciki har da tsohon Shugaban kasa Mohammed Nasheed da ke gudun hijira a kasar waje. Nasheed ne shugaban kasar na farko da aka zaba a dimokaradiyyance.
Facebook Forum